9 Mayu 2020 - 06:13
Jagora: Iran Za Ta Iya Samar Da Ci Gaba Na Kere-kere

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Bisa albarkatun da Iran take da su, za ta iya samar da ci gaba na kere-kere, kamar yadda ta sami nasarori a fagen kere tauraron dan’adam na masana’antu da kuma na tsaro.

(ABNA24.com) Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Bisa albarkatun da Iran take da su, za ta iya samar da ci gaba na kere-kere, kamar yadda ta sami nasarori a fagen kere tauraron dan’adam na masana’antu da kuma na tsaro.

Jagoran wanda ya gabatar da jawabi ta bidiyo dangane da shiga makon; Aiki da ma’aikata” ya kara da cewa; Za mu cimma wannan manufa, domin idan har za mu iya harba tauraron dan’adam mai cin mita 7,500 a cikin dakika zuwa sama, sannan kuma ya isa inda aka tura shi, to za mu iya samar da ci gaba ta fuskar kere-kere.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa; Tabbas wanda duk ya ke da wannan ruhin, to zai iya kera mota wacce za ta ci nisan kilo mita 100 da lita biyar na makamashi.

Jagoran ya yaba wa ma’aikata da masu samar da ayyukan yi domin su ne ginshikai biyu masu muhimmanci na tattalin arziki.


/129